Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana Ba Za Ta Koma Karkashin Asusun Lamuni Na IMF Ba: Ken Ofori-Attah


Tambarin asusun lamuni na duniya
Tambarin asusun lamuni na duniya

Masana a fannin tattalin arziki sun bayyana mabambantan ra'ayoyi game da halin tattalin arzikin Ghana, da kuma ko ya dace kasar ta koma karkashin asusun lamuni na duniya ko a'a. Wannan na zuwa ne bayan da gwamnatin kasar ta ce Ghana ba za ta koma ga IMF ba.

ACCRA, GHANA - Gwamnatin Ghana ta yi watsi da yiwuwar komawa ga asusun lamuni na duniya da ake kira IMF a takaice, ministan kudin kasar Ken Ofori-Attah ya ce Ghana na da abinda ake bukata wajen dorewar tattalin arziki.

Gwamnatin ta ce ta karbi basussuka na makudan kudi daga kasashen waje, a saboda haka sake karbar bashi daga asusun lamuni bai dace ba.

Gwamnatin ta kuma ce ta rage kashe kudade daga asusunta, kuma ta bullo da matakan tara kudaden shiga na cikin gida, kamar wanda ta ke kyautata zaton za ta samu a tsarin harajin E-levy da ta ke ganin zai taimaka wajen gyara gibin kasafin kudin da ake fama da shi. Sannan kuma za ta ci gaba da hulda da asusun lamunin wajen jin shawarwari idan bukatar hakan ta taso.

Sai dai batun ya sa kwararru a fannin tattalin arziki tafka muhawara a kan a koma ko kada a koma ga asusun lamunin.

Tsohon ministan kudi Dakta Kwesi Botwe, ba shi da ra’ayin komawa domin ya na da ra’ayi daya da gwamnati na cewa basussukan da ake bin ta sun yi yawa.

Shi ko Farfesa Godfred Bokpin, Malami a jami’ar kasuwanci ta Ghana, cewa ya yi da zarar ajiyar Ghana a kasashen waje ta ƙare zuwa wani mataki, ba su da wani zaɓi da ya fi zuwa asusun lamuni. Ya kuma ce Ghana ta kai matakin yanzu domin an fara gani a darajar kudin cedi.

Sarki Imrana Ashiru Dikeni masanin harkar tattalin arziki, bai da ra'ayin komawa asusun lamuni, domin kasar ta gwada a baya bai yi mata alfanu ba. Ya na mai cewa, Ghana ta mayar da hankali wajen kaucewa zuba kudade inda bai kamata ba.

Amma, Hamza Adam Attijjany, mai sharhi a kan tattalin arziki, ya na ganin komawa ga asusun lamuni shi ne mafi dacewa ga kasar domin wasu matakan da gwamnati ta dauka ba za su bada sakamakon da ake tsammani ba.

Ghana ta fice daga shirin bayar da lamunin ne shekaru kadan da suka gabata bayan kammala wani shirin tallafin kasafin kudi na dala biliyan baya.

Saurari rahoton Idris Abdullah Bako:

Ghana Ba Za Ta Koma Karkashin Asusun Lamuni Na IMF Ba: Ken Ofori-Attah
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:35 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG