Ministan kojo Oppong Nkrumah yace ya kamata a dauki matakin gaggawa domin kawo karshen cin zarafin 'yan jaridu a Ghana.
Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a garin Ho dake yankin Volta a wani taron horas da alkalai kan bukatar kare 'yancin fadin albarkacin baki da kare lafiyar 'yan jarida.
Ministan Ya cigaba da cewa, Idan ana son wadannan ayyukan da a zahiri, ya zama abin kunya ga dimokaradiyya, ya zama dole a hukunta wadanda suke cin zarafin ko muzgunawa 'yan jaridu da sauri ba tare da la'akari da wanda ya aikata ba.
Muryar Amurka ta zanta da wani lauya kuma malami a jami’ar koyar da aikin jarida a Ghana Zakaria Tanko Musah wanda yace akwai doka daga cikin babi na goma sha biyu na kundin tsarin mulkin kasar Ghana da ya hana cin zarafin yan jaridu.
Wannan dai shine karo na biyar da ake kai wa 'yan jaridu hari a Ghana tun a watan Janairun farkon wannan shekarar.
Yan jarida a Ghana sun shafe shekaru suna fuskantar hare-haren yayin da suke gudanar da ayyukansu
Kasar Ghana dai na daga cikin kasashe a duniya da a ka fi cin zarafin 'yan jaridu wanda ya sanya aikin jarida yake da matukar wahala da hatsari, duk da cewa kasar na kan tafarkin damokaradiyya da ya kamata a saukaka tare da gyara wasu al’amura.
Saurari cikakken rahoton Hauwa Abdulkarim cikin sauti: