Ghana Ta Haye Mataki Na Biyu Na Bunkasa Samar Da Makamashin Nukiliya

Taron makamashin nukiliya

Yayin da Ghana ta kammala mataki na biyu na bunkasa samar da makamashin nukiliya, gwamnatin Amurka da Japan sun kara jaddada alkawarin tallafa wa shirin makamashin nukiliyar Ghana, da ke da nufin ba da ingantaccen makamashi mai tsabta.

Wannan na daga cikin kokarinta na kara kiyaye gurbacewar yanayi da bunkasa masana’antu.

Mista Mochizuki Hisanobu, jakadan Japan a Ghana da Mista Dean Matlack, wakilin jakadan Amurka a Ghana, su ne suka jaddada alkawarin a wani taron kara wa juna sani kan samar da makamashin nukiliya na Ghana, wanda Hukumar Makamashin Atom na Ghana (GAEC) da Tsangayar Makamashin Nukiliya ta Kasa (NPI) suka shirya. A jawabinsa, Mista Dean Matlack ya ce:

"Gwamnatin Amurka ta dukufa kwarai wajen ganin nasarar shirin makamashin nukiliya na Ghana, kuma za mu ci gaba da yin aiki tare don tabbatar da cewa Ghana za ta iya kara karfin makamashin nukiliya cikin aminci. Muna matukar farin ciki game da kokarin da Ghana ke yi kan makamashin nukiliya kuma za mu kasance tare da Ghana a kowane mataki na gaba."

Taron makamashin nukiliya

Mista Hisanobu a nasa bangaren ya ce kasar Japan za ta ci gaba da tallafa wa kokarin da Ghana ke yi na cin gajiyar amfani da makamashin nukiliya cikin lumana ta hanyar yin la'akari da yiwuwar isar da fasahar nukiliya zuwa kasar. Ya kara da cewa:

"Don cimma burin hadin gwiwar kasashen uku, gwamnatin Japan tana ba da tallafi ga nazarin da kamfanoni masu zaman kansu na Japan, kamfanin IHI da na JGC suke yi tare da hadin gwiwar takwarorinsu na Amurka."

Taron makamashin nukiliya

Mataimakin ministan makamashi na Ghana, Andrew Kofi Egyapa Mercer, ya sanar da cewa Ghana ta kammala kashi na biyu na aikin samar da makamashin nukiliya na kasa, wanda ya hada da amincewa da inda za a samar da makamashin.

"A halin yanzu mun sami izinin mallakan nukiliya da muke bukata da kuma tanadin inda za a ajiye makamashin nukiliya na farko ta Ghana. Kuma biyan bukatunmu na makamashi ya zama tilas, don dorewar ci gaban masana'antu da tattalin arzikinmu, wanda ake bukata ga ci gaban kasa mai matsakaicin tattalin arziki."

Ya ce, duniya tana kaura zuwa mafi tsaftataccen tushen makamashi kuma ana hasashen nukiliya ce za ta zama tushen wannan makamashi mai mahimmanci, don haka ba za a bar Ghana a baya ba.

Mohammed Jafaru Dankwabia, shi ne mataimakin darektan cibiyar binciken canjin yanayi da kiyaye abinci, yace baya ga magance matsalar wutar lantarki, tabbatar makamashin zai taimaka wajen magance dumamar yanayi dake addabar Ghana da sauran kasashen duniya.

Baya ga saukin farashin wutar lantarki ga masana’antu da kuma samar da dubban aikin yi ga al’ummar Ghana, da makamashin nukiliya za ta kawowa Ghana, mai sharhi kan tattalin arziki, Hamza Adam Attijjany ya kara da cewa duk da yake ana kashe makudan kudi wajen assasawa amma gyara da tafiyar da shi na da sauki, kuma karkon makamashin ya sa yana daukar lokaci kafin ya lalace, domin haka, kasa ba za ta dinga zuba kudade da yawa wajen kula da gyara ba.

Kasar Amurka da Japan sun fara daukar alkawarin tallafa wa Ghana a shirinta na bunkasa makamashin Nukiliya a taron ministocin makamashin nukiliya na hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa da aka gudanar a birnin Washington DC, a watan oktoba 2022.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

Your browser doesn’t support HTML5

Ghana Ta Shiga Mataki Na Biyu Na Bunkasa Samar Da Makamashin Nukiliya