KUMASI, GHANA - Abin da masana suka ce wannan yunkurin zai taimaka ma kasar Ghana ta fannoni da dama ciki harda magance matsalar karancin wutar lantarki da samar ma kasar kudaden shiga tare da magance matsalar sauyin yanayi. Kuma Ghana zata zamo cibiyar bunkasa fasahar nukliya a nahiyar Afrika.
Kasashen sun bayyana hakan ne yayin wani taron makamashin nukiliya tsakanin ministocin kasa da kasa a birnin Washignton DC na kasar Amurka, taron da mataimakin ministan makamashi a Ghana Hon. William Owuraku Aidoo ya halarta.
Ministan harkar tattalin arziki da kasuwanci tare da masana'antu na kasar Japan, Ota Fusar, da ya fitar da sanarwar ya jadadda cewa a shirye suke su samar da wannan fasahar ta nukliya a Ghana saboda ci gaban da kasar ke samu wajen inganta shirye shiryenta na fasahar nukliya.
To ko shin meye fasahar nukliya ta SMR a takaice da Amurka tare da Japan zasu samar wa Ghana? Farfesa Adamu Idrisu Tanko masani kuma malami a Jami’ar Bayero a tarayyar Najeriya ya ce "wannan fasaha ta SMR hanya ce ta samar da makamashin nukliya kuma bata da hatsari na fidda iskar carbon dioxide kuma ba a bukatar wata fasaha tukunna a sanyaya su. Ana ganin wannan fasaha za ta kawo ci gaba a kasashen duniya saboda suna da dadin sha'ani musamman masana'antu ne da za a iya kera su wani guri kuma a tafiyar da su zuwa wani guri” inji shi.
Shi kuwa mai sharhi bisa harkar makamashi a Ghana kana babban lakcara a Jami’an Kwame Nkurmah da ke Kumasi Farfesa Abdul Rahman Muhammad ya ce wannan sabuwar fasahar muddun an samar da ita a Ghana za ta yi taimako sosai amma kuma kamata yayi da a horar da wadanda za su ringa kula da na’urar tare da wayar da kan al’ummar kasar domin samun amincewarsu tukuna.
Farfesan ya ci gaba da cewa ko shakka babu wannan fasaha zai taimaka wajen samar wa kasar kudaden shiga saboda Ghana zata iya samar wa makwabtanta wutar lantarki kamar yadda take yi ada.
Ghana zata zamo cibiyar nukliya tare da samar wa wasu kasashen ketare makamashi abin da ka iya farfado da tattalin arzkinta.
Saurari cikakken rahoton daga Hamza Adam: