Jami’an kasar Iran sun ce ana inganta makamashin uranium dinne domin makamashi da fararen hula ke amfani da shi, wanda bai kai karfin makamashin da aka amincewa da shi ba a cikin yarjejeniyar shekara ta 2015.
Mai yiwuwa ba da dadewa ba Iran zata zarce adadadin makamashin da aka bukaci ta adana a cikin wannan yarjejeniya.
Shugaban Iran Hassan Rouhani ya sanar a makwanni biyu da suka gabata cewa zai fice daga wasu bangarori na yarjejeniyar nukiliya tsakanin kasashe shidda, da ta hada da yanayin da Iran zata iya sayar da wani adadin makamashin uranium ga wasu kasashe.
Rouhani ya yi barazanar Iran zata iya kaiwa matsayin kera makamai da makamashin idan bata sami sassaucin tattalin arziki da aka yi mata a yarjejeniyar kafin farkon watan Yuli ba.
Shugaban Donald Trump ya fice daga yarjejeniyar nukiliyar shekara daya da ta gabata. Ya kuma sake kakabawa Tehran takunkumai kana ya yi barazanar kara wasu takunkuman a kan kasashe da suka ci gaba da kasuwanci da Iran. Shawarar da Trump ya yanke ta kara raunana tattalin arzikin Iran wanda dama yake fama da matsaloli.
Facebook Forum