ACCRA, GHANA - Bana Hukumar aikin Hajjin kasar Ghana ta kasa cike kwatar da kasar Saudiya da ba ta, saboda wasu dalilai da suka shafi tsadar kudin Hajjin na bana, inda wasu suka yi amfani da bisar ziyara domin yin aikin Hajji, wasu kuma sun shiga ta makwabtan kasashen kamar Nijar, Najeriya da Togo domin zuwa kasar Saudiya don yin aikin Hajjin na bana.
Shugaban Hukumar Hajin Ghana (Ghana Hajji Board) Alhaji Ben Abdallah Banda, ya tabbatar da hakan inda yake cewa Hukumar Saudiya dai kujera 6000 ta bayar wanda yake gani ba za’a iya kai wannan adaden ba, yana mai cewa, adadin da za su iya samu shi ne maniyata aikin hajji 4000 kawai
Ya kara da cewa, suna sa ran ya fi hakan kafin jirgin karshe ya tashi saboda, mutani na ci gaba da biyan kudin zuwa Hajji.
Alhaji Banda ya ce yarjejeniyar da Hukumar Hajjin Ghana tayi da masu jiragen sama da otel-otel, da masu ruwa da tsaki a jigilar maniyyata aikin Hajji, yana tsaye ne kan adadi da suka iya samu.
Shi kuma Shugaban masu sadarwa na aikin Hajjin Ghana Alhaji Abdul Rahman Gomda ya ce tsarin aikin Hajjin bana ba’a taba yin sa a tarihin aikin Hajjin Ghana ba.
Yayin tattaunawa da maniyyata aikin Hajjin bana wadanda suka tashi daga filin wasan jirgin sama na birnin Tamale dake Arewacin Ghana sun bayyana cewa shirye-shiryen bana yayi kyau.
Daya daga cikin maniyyatan Hajia Salamatu Alhaji Tahiru Ejura ta ce saboda fatan yadda suka samu komai cikin sauki daga Ghana, su samu saukin haka a kasar Saudiyan.
Alhaji Papa Angola wanda ya yi sama da shekara 20 yana fashin baki a kan aikin Hajjin Ghana, bana ma ya yi sokaci cewa, yana ganin Hukumar Hajjin Ghana ba zata iya kai adadin kwatar da ake bukata ta bana ba, idan har Saudiya bata hana bada visa ziyara ba kamar yadda Najeriya tayi.
Saurari cikakken rahoto daga Hawawu AbdulKarim:
Your browser doesn’t support HTML5