Ghana Ta Gargadi ‘Yan kasarta Kan Zuwa Birnin Abuja

Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo (AP)

A watan da ya gabata, Amurka, Birtaniya da wasu kasashen ketare suka fitar da sanarwa, inda suka yi kira ga ‘yan kasarsu da su yi hattara saboda akwai yiwuwar akai hare-haren ta’addanci a birnin na Abuja.

Gwamnatin Ghana, ta yi kira ga ‘yan kasarta da ke zuwa Najeriya da su guji zuwa Abuja, babban birnin kasar.

Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar a ranar Laraba, hukumomin Ghana sun ce sun fitar da wannan kashedi ne saboda yanayi na rashin tabbas da ake fuskanta a fannin tsaro a Abuja.

“Muna kira ga jama’a (‘yan Ghana) da su guji zuwa Abuja idan tafiyar ba ta zama dole ba, saboda yanayi na rashin tabbas a fannin tsaron birnin da ya danganci ayyukan ta’addanci, muggan ayyukan, rikicin kabilanci, hare-haren ‘yan bindiga da garkuwa da mutane.” Sanarwar ta ce.

A watan da ya gabata, Amurka, Birtaniya da wasu kasashen ketare suka fitar da sanarwa, inda suka yi kira ga ‘yan kasarsu da su yi hattara saboda akwai yiwuwar akai hare-haren ta’addanci a birnin na Abuja.

Hukumomin Najeriya sun yi watsi da sanarwar ta Amurka da Birtaniya kan yiwuwar kai hare-hare a Abuja inda suka ce babu wani abu makamancin haka.

Sai dai Ghana ta ce ta dauki wannan mataki ne lura da umarni da hukumomin Najeriya suka ba wasu otel-otel na su rufe harkokinsu.

“Idan har ya zama dole sai an yi tafiya zuwa birnin na Abuja, akwai bukatar a yi takatsantsan.

“Za mu ci gaba da sa ido kan lamarin, idan har yanayin na tsaro ya inganta, za mu sanar da jama’a.” Sanarwar mai dauke tambarin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Ghana ta kara da cewa.