Wannan ya biyo bayan dokar hana zirga-zirgar babur din ‘a daidaita sahu’ da aka fi sani da ‘Yellow yellow’, hanyar sufurin gama gari a yankin, da hukumar tsaron yankin sama maso gabas (REGSEC) ta gindaya domin kara matakin inganta tsaro.
A wata wasika mai dauke da sa hannun shugaban karamar hukumar, Abugri Busia, zuwa ga daraktan ilimi na gundumar, ta ce mambobin kungiyar na bakin cikin kalubalen tsaro da ake samu a yankin.
Wasikar ta ci gaba da cewa, “saboda rashin tsaro da kuma hana babura masu taya uku aiki, muna roko da a rufe makarantun boko a gundumar, har sai an samu ci gaba a harkar tsaro”. Babu tabbacin kare ran daliban makarantar da malamansu sakamakon sake barkewar rikici da aka samu a yankin.
Sheikh Musa Bagnya, limamin masallacin Azhariyya ne dake cikin Bawku, ya amince da wannan kira da majalisar shugabannin makarantu ta yi. Kamar yadda ya sanar da ni a wayar tarho cewa, ba a sanin lokacin da za a fara harba bindiga a garin, kuma idan an fara, kowa na rudewa ne; manya maza da mata na ta kan su. Lallai yara za su tagayyara.
Masani a kan harkokin tsaro da huldar kasa da kasa, Irbad Ibrahim yace duk da cewa gwamnati ta kawo wasu matakan tsaro, amma ya kamata ta kara, domin kasancewar kasar na da iyaka da Burkina Faso da take fama da tashin hankali, ana shigowa da makamai daga nan, kuma hannun matasa suke shiga.
Shin idan an rufe makarantun boko, ta ya ya zai shafi al’ummar Bawku? Malam Bashir Shehu, mai sharhi a kan harkokin ilimi yace lallai zai yi illa domin an kusa fara jarrabawar WASSCE na babban sakandare da BECE na karamin sakandare, kuma jarrabawa iri daya duk daliban Ghana za su rubuta. Yana kira ga gwamanti da ta gagguta daukar mataki.
Sai dai a wani jawabi mai dauke da sa hannun sakataren wata kungiyar gargajiyar Kugaug, Mista Mumuni Fuseini Azonko, ta ce keke mai kafa uku ya kasance hanyar samun kudin shiga ga matasan yankin, domin haka suna kira ga hukumar tsaro ta REGSEC da ta janye hukuncin hana su aiki da ta yi; za su bi duk dokar da aka gindaya musu.
Saurari rahoton Idris Abdullah Bako:
Your browser doesn’t support HTML5