Hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa, muddun ba a dauki mataki ba, to shigowar mayaka daga Burkina Faso na iya bai wa wasu 'yan ta'adda damar samun gindin zama a Ghana.
In kuwa ba a dau mataki ba, to shigowar mayakan daga Burkina Faso zai iya bai wa wasu yan ta'adda damar samun gindin zama a Ghana, inji hukumar 'yan sandan kasar.
Mallam Usman Muhammad Mansur, wakilin al'ummar zango a fadar sufeto janar din yan sandan kasar, ya tabbatar wa Muryar Amurka wannan bayani.
A nashi tsokacin, mai sharhi kan harkar tsaron ciki da wajen Ghana, Mallam Irbad Ibrahim, na ganin bai kamata Ghana ta alakanta rikicin kabilanci da 'yan ta'adda ba.
Muryar Amurka ta tuntubi magakujerar majalisar tsaron gundumar Bawku, Hon Hamza Amadu, wanda ya bayyana cewa, a bara wasu 'yan ta'adda na kasar Burkina Faso su ka kusanci Ghana, amma dakarun soja sun kora su kuma gwamnatinsa ta jamiyyan NPP na kokarin tsare iyakokin kasar
Bawku, dake jahar arewa maso gabashin kasar Ghana, na daga cikin garuruwa da harkokin kasuwanci ya bunkasa sosai, saboda gundumar na da iyakoki da kasashe biyu masu makwabtaka da Ghana, wato Togo da Burkina Faso.
Rikicin kabilancin na tilasa al'ummar yankin tserewa domin neman mafaka. A baya bayan nan sai da aka rufe makarantu da kasuwanni sakamakon rikicin.
Saurari cikakken rahoton Hamza Adams: