‘Yan wasan Ghana Black Stars za su kara da takwarorinsu na Comoros a ranar Talatar nan yayin da da ake ci gaba da fafatawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON a Kamaru.
Wannan ne wasan Ghana na karshe a rukuninsu na C inda take a matsayi na uku a teburin rukunin da maki daya tal.
A wasanta na farko, Ghana ta sha kaye a hannun Morocco da ci 1-0 yayin da ta yi kunnen doki da ci 1-1 da The Panthers of Gabon a ranar Juma’a.
Ba nasara kadai Ghana take bukata a wannan wasa da Comoros ba, har ila yau tana fatan daya wasan da za a buga a rukunin – wato wasan Morocco da Gabon ya zamanto wanda zai mata dadi.
Sai dai kamar yadda jaridar yanar gizo ta Football Ghana ta ruwaito, kocin kungiyar ta Ghana da Milovan Rajevac da kyfatin Andre Ayew sun ce suna da kwarin gwiwar za su kai ga gaci – wato zagayen ‘yan 16.
A nasu bangaren, ‘yan wasan Comoros karkashin jagorancin Amir Abdou ba kanwar lasa ba ne, mafi akasarinsu a Faransa suke kwallo.
Kungiyar ta Comoros wacce ake wa lakabi da Les Coelacantes, na da zaratan ‘yan wasa irinsu Ali M’Madi, Youssouf M’Changama da El Fardou Ben Nabouhane da za su iya shammatar Ghana.
Wannan shi ne karon farko da Ghana da Comoros za su hadu a gasar ta AFCON kamar yadda AP ya ruwaito.