WASHINGTON, D.C. —
Kasar Afrika ta Kudu na alhinjn mutuwar dan gwagwarmayar yaki da wariyar launin fata baban Lauya George Bizos, wanda ya yi suna wajen kare tsohon shugaban kasar marigayi Nelson Mandela.
A cewar iyalan Bizos ranar Alhamis 10 ga watan Satunba, marigayin wanda aka haifa a kasar Girka, ya je Afrika ta Kudu ne a matsayin dan gudun hijira a lokacin yakin duniya na 2, ya rasu a jiya Laraba a gidansa yana da shekaru 92 a duniya.
A wani jawabi da Shugaban Afrika ta Kudu Cyral Ramaposa ya yi, ya bayyana margayi Bizos a matsayin “Mikiyar kasar ta fannin shari'a."