A yau litinin 18 ga watan Yuli ake bukin ranar tunawa da tsohon shugaban Afirka ta Kudu, kuma madugun yaki da wariyar launin fata, Nelson Mandela, a duk fadin duniya.
Marigayi Nelson Mandela, wanda ya mutu yana da shekaru 95, ya shafe kusan tsawon shekarun rayuwarsa yana hidima ga al'umma a matsayinsa na lauyan kare hakkin bil adama, tsohon fursuna, kuma mai fafutukar wanzar da zaman lafiya da kuma shugaban dimokuradiyya na farko a kasar Afrika ta kudu bayan kawo karshen wariyar launin fata a kasar.
Majalisar dinkin duniya tayi la'akkari da irin rawar da ya taka ta fuskar 'yancin bil adama da yafe ma juna, da kawo daidaito a tsakanin al'ummar kasarsa. Wannan dalilin ya sa Majalisar ta fadada bukukuwan ranar tunawa da Mandela domin ta kunshi ayyukan jinkai da tausaya wa al'umma, musamman fursunoni da kuma wayar da kan jama'a game da muhimmancin ma'aikatan kurkuku.
Ga rahoto na musamman daga bakin Mahmud Ibrahim kwari kan wannan rana ta musamman ta tunawa da Nelson Mandela.