Shugaba Mandela ya kwashe shekaru 27 a wani mugun gidan kaso dake tsibirin Robben domin fafitikar da ya yi da gwamnatin wariyar launi da ta mayar da bakake tamkar dabbobi marasa wani anfani illa su bautawa fararen fata.
Bayan an sanarwa duniya rasuwarsa mutane a kasashe daban-daban sun fadi albarkacin bakinsu dagane da marigayin. A Najeriya mutane da dama sun fadi nasu ra'ayin kan marigayin. Malam Sidi Ali tsohon dan siyasa shi ma wani dan gwagwarmaya da mulkin kama karya a Najeriya ya san duk wasu 'yan gwagwaryamayar Afirka. Kafin Nelson Mandela ya taso bakin tamkar bawa yake.Nelson Mandela da ya tashi ya kawo mutane daga kabilu daban daban ya hada kansu domin su yaki mulkin wariya. Ya kawo mutane kamar su Oliver Tambo da wasu su yi aiki tare. Wadanda suka yi gwagwarmaya tare ya debosu ba kan kabilanci ba. Mandela ko a mace ko a raye ya kafa tarihi a Afirka.
Shi kuma Buba Galadima babban sakataren jam'iyyar CPC da ta narke zuwa cikin APC ya ce Nelson Mandela yana daya daga cikin gwarzayen duniya gaba daya wadanda suka sadakar da kansu domin al'ummarsu. Shi ne wanda ya gwammace ya yi iyakar rayuwarsa a gidan kaso domin ya ki ya sayar da 'yancin al'ummarsa. Ya yi watsi da nashi 'yancin kansa sai tare da na al'ummarsa. A duniyar nan mutane kalilan za'a iya kwatanta halayensu da na Nelson Mandela kamar su Mahatma Ghandi na Indiya. Nelson Mandela ya samu cikakken yabo daga duk mutanen duniya. Yakai dattijo a koina domin ya yafe ma wadanda ma suka sa shi gidan kaso na tsawon shekara 27. Buba Galadima ya ce ya je inda aka tsareshi da inda a ke sasu sarar dutse dare da rana. Domin matukar son al'ummarsa babu wata wuya da ya taba shiga da ta sa ya canza 'ra'ayinsa.
Shi ma tsohon shugaban EFCC Nuhu Ribadu ya ce Madiva kamar yadda mutanen Mandela ke kiransa ya yi rayuwar sadakar da kansa ma al'ummarsa. Ya jimre wahala. Babu wata wahala da bai sha ba. Ya yaki zalunci da mulkin danniya. Ya yaki rashin gaskiyar turawan kasar. Amma Allah ya taimakeshi ya rayu har ya zama
shugaban kasar.
Ga cikakken rahoto.