Nelson Mandela, ya kwashe shekara da shekaru yana gwagwarmaya domin kawo samun ‘yancin kasar daga turawan mulkin mallaka da kuma kawo karshen nuna banbanci da wariyar launin fata, ko yaya wasu ‘yan Najeriya ke ganin wannan jan gwarzo?
Jama’a da dama sun bayyana ra’ayoyin su musamman ganin yadda wannan shugaba ya sha gwagwarmaya domin kwatarwa kasar sa ‘yanci daga turawan mulkin mallaka.
Idan aka kwatanta tarihinsa da ci gaban da kasar ta Afirka ta kudu ta samu, akwai darussa da dama da suka kamata shugabannin kasashen Afirka, su yi koyi da su, ganin yadda har kasa ta nade baza a taba mantawa da shi ba.
Taken bukin na wannan shekarar shine tashi tsaye domin yaki da talauci da kuma tabbatar da dai-daito ko adalci a tsakanin al’ummar duniya baki daya.
Daga Legas wakilinmu Babangida jibrin da da karin bayani.
Facebook Forum