Gasar Kofin Duniya: Ivory Coast Ta Doke Gambia 2-0

Magoya bayan Ivory Coast

A gefe guda kuma, Djibouti ta karbi bakuncin Guinea-Bissau a birnin Alqhira, inda ta sha kaye da ci 1-0.

Ivory Coast ta lallasa Gambia da ci 2-0 wasan neman gurbin shiga Gasar cin Kofin Duniya a ranar Litinin.

Dan wasan gaba Christian Kouame da dan wasan tsakiya Seko Fofana ne suka zura wa Ivory Coast kwallayenta a Tanzania, kasar da Gambia ta zaba ta zama mata gida.

Wannan nasara ta biyo bayan lallasa Seychelles da ksar ta yi da ci 9-0 a Abidjan a ranar Juma’a.

Rabon da Ivory Coast ta je gasar kofin duniya tun a shekarar 2014, wanda shi ne karo na uku da take halarta.

A gefe guda kuma, Djibouti ta karbi bakuncin Guinea-Bissau a birnin Alqhira, inda ta sha kaye da ci 1-0.

Wannan kayen na zuwa ne kwana hudu bayan da ta sha kaye a hannun Masar da ci 6-0.

Canada, Amurka da Mexico ne za su karbi bakuncin gasar kofin duniya ta FIFA a 2026.