Ganduje Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Ta Bude Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano

Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sake bude filin tashin jiragen sama na Mallam Aminu Kano.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da tawagarsa sun kai ziyarar neman gwamnatin tarayya ta sake bude ayyukan zirga-zirgar kasa-da-kasa na fasinjoji a filin tashi da saukar jiragen saman Mallam Aminu Kano da sabon filin tashi jiragen na Murtala Muhammad da aka kusan gama aikisa a jihar Kano.

A cikin watan Satumbar shekarar 2020 ne gwamnatin Najeriya ta sake bude ayyukan jigilar fasinjojin kasa da kasa, bayan kasancewa a rufe na tsawon watanni 6 domin dakile yaduwar annobar Coronavirus da ta yi mummunar tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Ministan sufurin jiragen saman Najeriya Hadi Sirika, ya bayyana cewa, tattaunawa a kan sake bude zirga-zirgar kasa da kasa a filin tashi da saukar jiragen saman Mallam Aminu Kano da na sabon filin jiragen na Murtala Muhammad, ya yi armashi.

Mallam Sirika ya ce game da batun bai wa masu zuba jari daga ciki da wajen Najeriya daman shiga a dama da su wajen bunkasa fannin sufurin jiragen saman Najeriya, ba za ayi kamar na baya ba.

A watannin baya-bayan nan 'yan kasuwa da Masu fada a ji a Jihar ta Kano su ma sun yi kira ga gwamantin da maido da harkokin sufurin jiragen saman kamar yadda aka maido da sauran na sassan kasar.

Kano ta kasance babbar cibiyar kasuwanci a Najeriya musamman a arewacin kasar

A saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulra’uf:

Your browser doesn’t support HTML5

Ganduje Ya Yi Kira Ga Gwamnatin Tarayya Da Ta Bude Filin Jirgin Sama Na Malam Aminu Kano