Tun bayan da ofishin jakadancin na Amurka ya fitar da hotuna da ke nuna Sarkin Fulanin Yanmacin Najeriya, Muhammadu Babbado na ganawa da jami’an ofishin Jakadancin Amurka ta shafin yanar gizon ofishin ne ‘yan Najeriya, musanman al’ummar yankin yanmacin kasar, ke ci gaba da maida martani a kan wannan ganawar.
Wasu dai na da ra’ayin cewa kamata ya yi jami’an na Amurka su gana da Sarkin Legas, a maimakon na Fulani, musanman a wannan yanayi da ake zaman doya da manja tsaknin Fulanin da al’umar kudancin kasar.
Karin bayani akan: Alhaji Ado Dansudu, Fulanin, Fulani, Nigeria, da Najeriya.
Alhaji Salihu Ba-shankai shi ne mataimakin ba-saraken Fulanin a yankin yanmacin Najeriya kuma ya kare matakin ganawar da Sarki Babbado ya yi da jami'an jakadancin na Amurka, wanda ya ce an yi domin tattauna hanyoyin samun zaman lafiya tsakanin Fulani da abokan zamansu na Najeriya, ciki har da Yarbawa.
Koda yake kokarin samun martani daga ofishin jakadancin na Amurka bai yi nasara ba, a sanarwar da ta fitar tun da farko, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ta ce an shirya ganarwar ne domin samo bakin zaren warware rigingimun Fulani da manoma a yankin kudancin kasar da ma kasa baki daya. Kuma irin wannan ganawar ake bukata a halin da kasar ta samu kanta a ciki, kuma a shirye ofishin jakadancin na Amurka yake ya gudanar da irin wannan ganawa da bangarori daban daban a nan gaba.
Alhaji Ado Dansudu, shugaban wata kungiyar ci gaban ‘yan Arewacin Najeriya ne, wanda kuma ya maida martani game da wannan ganawa, yana mai cewa ganawar ba wani sabon abu bane.
Yanzu dai a yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da muhawara a kan wannan ganawa, bangaren masarautun Fulanin na kira a samu fahimtar juna domin kawo karshen rigingimun Fulani da ‘yan kasa, kamar yanda Sarkin Fulanin Shagamu, Salisu Ba-shankai ya sheda wa Muryar Amurka.
Ga dai rahoton Babangida Jibrin daga birnin Iko a Najeriya:
Your browser doesn’t support HTML5