Shugaban kasar Gunea Alpha Conde da takwaransa na Mauritania Mohammed Ould, suna babban birnin Banjul domin ganawa da shugaba Yahya Jammeh.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afrika ta Yamma ECOWAS ko kuma CEDEO ta baiwa shugaba Yahaya Jammeh da ya sha kaye a zaben shugaban kasar da ya mika mulki ya bar kasar ko kuma tayi amfani da karfin soji ta sauke.
Mu dakatar da harkoki kuma mun bashi lokaci ya bada mulki inji Marcel Alain de Souza shugaban kwamitin zantarwa na ECOWAS, ya kuma kara da cewar idan karfe 12 na rana bai mika mulki ya bar kasar Gambia ba, sojojinmu zasu shiga ciki.
De Souza yace a kwai rundunoni dubu bakwai dake jibge a Senegal da wasu kasashe hudu da zasu shiga kwana daya bayan sojojin sun shiga Gambia.
Shugaba Guinea Alpha Conde shine zai jagoranci tattaunawar karshe a babban birnin kasar Banjul da safiyar yau Jum’a a cewar de Souza
Kwamitin sulhu na MDD ya riga ya tabbatar da Adama Barrow a matsayin sabon shugaban Gambia, a yayinda dadadden shugaban kasar Jammeh yaki sake mulki.