Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsananin Fari Ya Sa Somalia Na Rokon Duniya Ta Tallafa Mata


Awakai da suka mutu sanadiyar tsananin fari
Awakai da suka mutu sanadiyar tsananin fari

Saboda masifar farin da ya sake abka mata a karo na biyu, gwamnatin kasar Somalia ta fito fili, tana rokon duniya da ta taimaka mata da agajin da zata tallafa wa al’ummarta, kada yunwa ta hallaka su, su da yawa.

A lokacinda yake ganawa da manema labarai tareda ‘yan Kwamitin Yaki Da Fari da ya kafa, shugaban kasar ta Somalia, Hassan Shiekh Mohamud yace milyoyin mutanen kasar tashi ne ke fuskantar mutuwa daga yunwa in ba duniya ta hanzarta kawo musu dauki ba.

Shugaban yace yanzu haka yunuwa ta riga ta kashe dimbin mutane masu yawa dake da rauni kamar mata da kananan yara, kuma su ma masu dan karfi-karfin, yanzu sun fara kasawa.

Tun ranar Talata ne jami’in Cibiyar Samarda Agaji ta MDD ya fadi cewa mutanen Somalia kamar milyan biyar ne, ko rabin daukacin dukkan mutanen kasar, ke fama da karancin abinci saboda Fari a sanadin rashin samun ruwan sama, sa’annan ga kuma rashin zaman lafiyar da ake fama da shi a sanadin yakin da har yanzu ake gwabzawa tsakanin sojan gwamnatin da mayakan al-Shebab.

Shi kuma babban Darektan Ma’aikatar Harakokin Cikin Gida na Somalia din, Yahye Ali Ibrahim, yace yanzu haka mutane milyan 2.7 ne ke gab da mutuwa saboda rashin cimakar.

XS
SM
MD
LG