A jiya Alhamis ne aka rantsarda Adama Barrow a matsayin sabon shugaba a wani shagalin da aka gudanar a Opishin Jakadancin Gambia dake kasar Senegal. Kamata yayi ace a birnin Banjul aka rantsar da shi amma saboda yadda abubuwa suke, tilas aka chanja.
Wani hafsan sojan kasar ta Senegal ya gaya wa kampunnan watsa labaran Yammaccin Turai tun jiya cewa tuni sojan Senegal suka tsallaka zuwa cikin Gambia din, yayinda wani jam’in gwamnatin Nigeria ya tabattarda cewa su ma sojan Nigeria din suna cikin wannan yunkurin na tabattarda zaman lafiyar Gambia.
Izuwa yanzu dai ba wani rahoto dake nuna cewa ana wani tashin hankali a Gambia.
Kakakin Ma’aikatar harakokin Wajen Amurka John Kirby yace Amurka na goyon bayan wannan matakin anfani da karfin soja da kasashen Afrika ta Yamma suke dauka akan Gambia.