Gamayyar Kungiyoyin Kwadago Ta Yi Barazanar Fara Yajin Aiki A Ghana

Kungiyoyin ‘Yan Kwadago A Ghana Sun Yi Barazanar Fara Yajin Aiki

Gamayyar kungiyoyin kwadago a Ghana sun bukaci gwamnati da ta janye matakin da ta dauka na shigar da kudaden fanshon ma’aikata a cikin shirin musanya basussukan cikin gida a wani bangare na sharrudan da hukumar ba da lamuni ta IMF ta shimfida ga kasar ko kuma su shiga yajin aiki.

KUMASI, GHANA - Sakatare Janar na gamayyar kungiyoyin kwadago ta TUC Dakta Yaw Baah ne ya bayyana hakan yayin da kungiyoyin da suka hada da na ma'aikatan kiwon lafiya na kasa wato GMA da GRNMA da malaman boko na kasa wato GNAT da NAGRAT tare da TEWU da wasu kungiyoyin ma'aikatan karkashin gwamnati suka gana da manema labarai.

Kungiyoyin sun jaddada cewa ma'aikata a kasar duk za su fara yajin aiki daga ranar 27 ga wannan watan nan Disamba kuma ba za su daina ba sai in gwamnati ta cire wannan kudaden fanshon na ma'aikatan karkashin shirin musanya basussukan cikin gida karkashin sharuddan IMF.

Kungiyoyin kwadagon sun bayyana cewa wannan mataki da gwamnati ta dauka zai janyo wa ma'aikata da suka yi ritaya matsala babba, saboda haka ba za su amince da shi ba.

Shariff Abdulsalam mai sharhi bisa lamurran yau da kullum ya fadawa Muryar Amurka cewa matakin da gwamnati ta dauka zai janyo kunci ga rayuwar ma'aikata musamman wadanda suke ritaya tare da bukatar bangarori biyun su zauna domin cimma daidaituwa.

Ahmad Badawi, daya daga cikin masu magana da yawun gwamnati ya ce ko shakka babu wannan matsala ce babba amma kuma halin da Ghana ta tsinci kanta a ciki yanzu, kamata ya yi a zauna tsakanin bagarori biyun, abin da ya ce an yi na farko tsakanin gwamnati da ‘yan kwadagon ba a samu dace wa ba.

Ahmad Badawi ya yi kira ga ma'aikatan da su kwantar da hankalinsu, ya na so a sake zama domin cima daidaito.

Sai dai ba shigar da kudaden fanshon ma'aikata kadai ne matakan da gwamnatin Ghana ta dauka ba, ciki ha rda dakatar da shirin biyan basukan da kasashen ketare ke bin ta.

Bayan tattaunawar da ta kaiga kulla yarjejeniya tsakanin IMF da Ghana mai fama da matsalar tattalin arziki, asusun ya gindayawa kasar sharrudan dakatar da biyan basukanta na ketare don samun damar murmurewa daga koma bayan da kasar ke gani ta fannin tattalin arziki.

Ministan tattalin arziki a Ghana na ganin wannan mataki na tinkarar asusun IMF ya taimaka wa kasar ta farfado daga matsalar da take fuskanta, amma sai da juriya saboda matakan da ake dauka ya shafi kowa a kasar.

Saurari cikakken rahoto daga Hamza Adam:

Your browser doesn’t support HTML5

Gamayyar Kungiyoyin Kwadago Ta Yi Barazanar Fara Yajin Aiki A Ghana.mp3