UKGBC wani babban taro ne da aka samar a shekarar 2018, domin habbaka dangantakar kasashen biyu da hadin gwiwa tsakanin kamfanoni masu zaman kansu na Ghana da takwarorinsu na Burtaniya.
Mataimakin shugaban kasa, Dakta Mahamudu Bawumia da Rt Hon Andrew Mitchell, Karamin Ministan raya kasa da Afirka ne suka jagoranci zaman tattaunawar a fadar shugaban kasa ta Jubilee Square.
Da yake jawabi a wurin zaman tattaunawar, Dakta Mahamudu Bawumia, ya yaba da gagarumin ci gaban hadin gwiwa da aka samu a karkashin majalisar kasuwanci tsakanin Burtaniya da Ghana (UKGBC) tun lokacin da aka kafa ta.
Ya ce manufarsa ga majalisar, na rage shingen kasuwanci da inganta hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Ghana da Birtaniya, ya kai ga samar da kudaden gudanar da wasu manyan ayyukan samar da ababen more rayuwa a fadin kasar da suka hada da: Filin sauka da tashin jirgin saman kasa da kasa na Kumasi, da na Tamale, Asibitin Yankin Gabas, dakin haihuwa da kula da yara a Asibitin Koyarwa na Komfo Anokye a Kumasi, kamfanin Aqua Africa Limited wanda ke samar da ruwa mai inganci ga garuruwa 16 a fadin kasar da sauransu.
Dakta Bawumia ya godewa gwamnatin Burtaniya, kuma ya bukaci a samu Karin hadin gwiwa a bangaren sauyin yanayi.
Rt Hon Andrew Mitchell, karamin ministan raya kasa da Afrika na Birtaniya, ya jaddada muhimmiyar rawar da majalisar ta taka wajen kara dankon zumunci tsakanin kasashen biyu. Haka kuma ya yi alkawarin kara hadin gwiwa mai zurfi ta hanyar kasuwanci, zuba hannun jari, tallafawa ci gaba mai dorewa da samar da aikin yi.
Masani a kan hulda tsakanin kasa da kasa, Irbad Ibrahim, ya nuna cewa lallai irin wannan hadin gwuiwar kasuwanci da kasashen yamma yana dorewa ko da kuwa an samu canjin mulki.
Ghana ce kasa ta hudu da Burtaniya tafi shigar da kayayyakin kasuwancinta a a kasa da hamadar Sahara, don haka Birtaniya ke da burin bunkasa kasuwancinta da Ghana zuwa fam biliyan 1.4 nan da shekarar 2024.
Domin Karin bayani saurari rahotan Idris Abdullah Bako: