Gamayyar Darikan Kristoci Ta Bukaci Samar Da Tsaro A Wuraren Da Rikici Ya Shafa

Taron Gamayyar Krista na jihar Filato

Gamayyar darikun mabiya addinin Kirista sun bukaci hukumomi su samar da tsaro a wuraren da rikici ya shafa a wasu kauyukan jihar Filato, don ba wadanda ke gudun hijira damar sake gina gidajensu su koma.

JOS, NIGERIA - Shugaban gamayyan darikun na Kirista kuma Shugaban darikar ECWA, Rev. Stephen Panya Baba, wanda ya jagoranci dukkan darikun zuwa kai tallafi wa 'yan gudun hijira da hare-haren 'yan bindiga ya rabasu da muhallansu a karamar hukumar Bokkos na jihar, ya bayyana takaicinsa kan yadda mutane fiye da dubu goma ke murkususu a sansani guda, tun fiye da wata daya, saboda rashin tsaro ya hana su komawa kauyukan su.

Wasu mutane da suka rasa matsugunansu saboda rikici a jihar Filato

Sansanin na cikin garin Bokkos na dauke da mutane fiye da dubu goma sha tara, banda wadansu sansanoni goma sha biyu a wurare daban-daban a karamar hukumar ta Bokkos.

Wasu mata da Muryar Amurka ta zanta da su, sun shaida cewa babbar matsalarsu itace su samu abinci su kuma samu tsaro don komawa kauyukansu suyi noma.

Mutane da suka rasa matsugunansu sakamakon rikici a Filato

Shugaban kungiyar mata Kirista ta CAN a jihar Filato, Madam Sarah Dalut ta gargadi matan ne kan su kare mutuncinsu.

Shima Shugaban kungiyar CAN a karamar hukumar Bokkos, Rev. Stephen Asugum ya ce suna bukatar kayan gine-gine don sake gina muhallansu.

Mata na Gamayyar Krista na jihar FIlato

Bayanai dai na nuni da cewa Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya amince da gina barikin soji a yankin Mbar na karamar hukumar Bokkos don tabbatar da tsaro a yankin.

Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji:

Your browser doesn’t support HTML5

Gamayyar Darikan Kristoci Ta Bukaci Gudunmawa Wa ‘Yan Gudun Hijira Daga Kauyukan Jihar Filato.mp3