Ga dukkan alamu dan wasan Napoli Victor Osimhen ya samu mafaka bayan da kungiyarsa ta amince ya tafi Galatasaray da ke kasar Turkiyya a matsayin dan wasan aro.
An yi ta kai ruwa rana a yunkurin dan wasan na ficewa daga Napoli kafin a rufe kasuwar cefanen ‘yan wasa.
Chelsea ta Ingila da Al Ahly da ke Saudiyya sun nuna sha’awar sayen dan wasan, sai dai lamarin ci tura.
Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa Paris Saint Germain ma ta yi zawarcin Osimhen.
A ranar 31 ga watan Agusta aka rufe kasuwar musayar ‘yan wasan a mafi aksarin kasashen turai.
Rahotanni sun ce Osimhen, wanda asalin dan Najeriya ne ya ki amincewa da tayin da Chelsea ta yi na pam miliyan 4 a daukacin kakar wasan, kudin da ya gaza matuka da pam miliyan 10 da Napoli take biyansa.
A Al Ahli kuwa, Osimhen ya amince da tayin pam miliyan 30 a daukacin kakar wasan, sai dai Napoli ta nemi karin pam miliyan 5 a matsayin kudaden alawus, lamarin da ya ruguza cinikin.
Hakan ya sa Osimhen ya shiga tsaka mai wuya domin har kungiyarsa ta Napoli ta fitar da jerin ‘yan wasanta na farko kuma ba ya ciki.
Ita dai kasuwar cefanen ‘yan wasa ta Turkiyyar tana bude har zuwa 13 ga watan Satumba.
Kuma faduwa ta zo daidai da zama domin kungiyar ta Galatasaray na bukatar dan wasan gaba na tsakiya.
A cewar kamfanin Dillancin Labarai na AP, kungiyar ta Galatasaray ta ce “dan wasan da kulob din SSCN Napoli sun fara tattaunawa kan sauya shekara dan wasa Victor Osimhen a mataki na wucin gadi.”