Ga Jigajigan ‘Yan Wasan Kwallan Kafa Da Suka Kamu Da COVID-19
Mohammed Salah, Liverpool - Striker
Rahotanni daga kasar Masar na cewa dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Mohammed Salah ya kamu da cutar COVID-19.
Cristiano Ronaldo, Juventus - Forward - Left Winger
Cristiano Ronaldo, daya daga cikin manyan tauraruwar kwallon kafa kuma daga cikin shahararrun ‘yan wasa a duniya, gwaji ya tabbatar cewa ya kamu da cutar coronavirus, kungiyar kwallon kafa ta Portugal ta sanar a ranar 13 ga Oktoba
Dan wasan gaban na Juventus mai shekara 35 yana cikin koshin lafiya, kuma ba shi da alamun cutar a cewar kungiyar.
Zlatan Ibrahimovic, AC Milan - Striker
Dan wasan gaba na AC Milan Zlatan Ibrahimovic ya kamu da coronavirus a watan Satumba yana mai cewa, "COVID na da karfin gwiwar kama ni”
Ya murmure daga cutar, ya kuma buga wasa da Inter Milan a cikin Derby della Madonnina a Oktoba 17.
Kylian Mbappé, PSG - Forward - Striker
Kungiyar ƙwallon ƙafa ta Faransa (FFF) ta tabbatar a farkon watan Satumba Paris Saint-Germain da ɗan wasan gaban Faransa Kylian Mbappé an tabbatar sun kamu da COVID-19.
Mbappé ya murmure sannan ya dawo wasa, ya kuma zura kwallaye a wasa tsakanin PSG da Nice, da ci 3-0.
Neymar, PSG - Forward
Tauraron dan kwallon kafar kasar Brazil Neymar yana daya daga cikin ‘yan wasan Paris Saint-Germain da suka kuma cutar COVID-19, a cewar rahotanni da yawa.
Neymar ya samu lafiya daga cutar sannan ya dawo tirenin tare da PSG a tsakiyar watan Satumba.
Paulo Dybala, Juventus, Forward - Second Striker
Dybala ya kamu da COVID-19 a cikin tsakiyar barkewar annobar ta duniya a Italiya.
Dybala ya sake fara atisaye a karshen watan Maris bayan ya murmure daga rashin lafiyar.
Callum Hudson-Odoi, Chelsea, Forward - Left Winger
An bada sanarwar cewa dan wasan gefe na Chelsea Callum Hudson-Odoi ya kamu da COVID-19. Hudson-Odoi shine dan wasan kwallon kafa na farko a Firimiya da aka tabbatar da kamuwa da cutar.
Dan wasan gefe na Chelsea ya 'murmure sosai' daga coronavirus a ƙarshen Maris.
Paul Pogba, Manchester United - Midfielder
An cire dan wasan tsakiya na Manchester United Paul Pogba daga cikin tawagar Faransa da za ta buga gasar UEFA Nations League a karshen watan Agusta bayan da gwaji ya nuna cewar ya kamu da cutar coronavirus.
Pogba ya koma horo tare da Manchester United a tsakiyar watan Satumba.
Mikel Arteta, Arsenal - Manager
Manajan Arsenal Mikel Arteta ya kamu da cutar COVID-19 a ranar 12 ga Maris, a cewar wata sanarwa a shafin intanet na kulob din. Ya samu lafiya, sannan ya dawo aiki tare da kungiyar ta Premier.
Sadio Mane, Liverpool - Forward
Dan kwallon Senegal Sadio Mane ya kamu da cutar ta coronavirus a farkon watan Oktoba lokacin wasan zakarun Premier na Ingila.
Kwanan nan Mane ya dawo horo bayan tsawon lokacin keɓe kansa.