Tun bayan bada wa'adin tada makiyaya daga daji da gwamnatin jihar Ondo ta yi, wasu fulani suka fara kaura zuwa arewacin Najeriya don neman matsuguni a bangarori daban daban.
Shugaban kungiyar Miyatti Allah na jihar Kaduna, Alhaji Haruna Usman Tugga, ya ce yanzu akwai fulani makiyaya su 150 da kuma iyalansu da suka kai kusan dubu hudu da suka yi kaura zuwa Kaciya ta kudancin jihar Kaduna.
Tugga ya kara da cewa wuraren kiwo za su yi karanci saboda babu wurin kiwo da yawa kuma ya nuna damuwar su na abin da wadannan Fulani za su ci, ga shi kuma suna da yara kanana.
Sannan ya yi kira da a taimaka musu daga nan kuma sai a yi shawara a duba mai ya kamata a yi domin wurin zai cika dam a rasa yadda za a yi.
Tuni dai wannan tururuwar fulani zuwa kudancin jihar Kaduna ya fara kawo fargaba ganin yadda yankin ke yawan fama da rikice-rikice.
Sai dai masani tsaro a Najeriya, Manjo Yahaya Shinko mai ritaya ya ce akwai aiki musamman ga hukumomi a arewacin Najeriya, kuma har ila yau za su iya amfanin da wannan dama wajan samar da zaman lafiya duk da yankin na kudancin jihar Kaduna ya dade yana fama da wannan rikice-rikice da fulani da wadan su kabilu.
Shinko ya kara da cewa kasancewar wadannan fulani masu tarin yawa da suka zo wannan gari zai iya yiwuwa su wadannan ‘yan gari idan sun karbe su an yi zaman lafiya da su sanadiyar su sauran fulani da ke zuwa daga waje suke kawo farmaki yanzu za su iya dainawa.
“Ko kuma ya Allah duk wadannan fulani da suka yo kaura suka dawo wurin suka sa baki a bari abin da ake yi gashi yanzu wadanan mutane sun karbe mu ko kuma ya Allah a a kasancewa da kansu yanzu ganin ga ‘yan uwansu sun zo wannan wuri suna iya dain kawo wannan farmaki,” a cewar Manjo Shinko.
Manjo Shinko ya ce “Dole gwamnati ta tashi tsaye musamman tun da sun riga sun zo tun yanzu a nemi shugabannin su a zauna da su a nuna musu zaman lafiya ake so ayi, matukar ba za su yi zaman lafiya a nan ma ba za a kyale su yi yadda suke so ba.”
Wannan matsala ta barazanar koro Fulani dai ta sa wasu gwamnatochin Arewa yanke shawarar tsara kiwon Zamani ta hanyar turke Fulani guri guda da kuma sama kayan more rayuwa abun da wasu ke ganin aiki ne da ka iya daukar lokachi.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5