Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Arewa Sun Fara Maida Martani Ga Korar Fulani Daga Kudancin Najeriya


Shanun Fulani Makiyaya
Shanun Fulani Makiyaya

A daidai lokacin da matsin lamba ke kara yawaita a kan fulani makiyaya su fice daga kudancin Najeriya, ‘yan arewa sun ce ai dama sakacin gwamnatoci ne ya kawo hakan domin arewa ta wuce ayi mata gori da fadin kasa mai dausayi da tsiro wadda kan iya wadatar da makiyaya.

Matsalar ayukkan ta'addanci da akasari akan alakanta fulani da ita, bata rasa nasaba da abin da yasa matsin lamba ya yi yawa a kan fulani su fice daga kudancin Najeriya.

A cikin hirar shi da Muryar Amurka, farfesa Ibrahim Mustapha Dankane masani a fannin yanayin kasa da muhalli a jami'ar Usmanu Danfodiyo dake Sakkwato na ganin cewa,duk da yake tsarin kasa ya baiwa kowane dan kasa damar zama duk inda yake so, ai arewa tana da dukan abinda Fulanin ke nema domin kiwon dabbobin su, inji

Dama tun kafin wannan barazanar da ake yi wa fulani wasu gwamnatoci a arewa sun fara shirin tsugunar da fulanin wuri daya don kaucewa yawace yawacen neman kasar kiwo kamar yadda gwamnatin Zamfara ta yi abin da wani jigo a kabilar fulani a Najeriya Muhammad Dodo Oroji ya ce abin Yabo ne.

Gwamnatin Sakkwato ma ta ce ba'a bar ta a baya ba a kan samar wa fulani abubuwan da suke bukata domin kange su daga zuwa yawon kiwo yankin kudu, acewar kwamishinan kula da lafiyar dabbobi na jihar Farfesa Abdulkadir Usman Junaidu.

Saurari rahotan Muhammad Nasir cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG