Shugabannin Fulani a jihar Neja sun ce lamarin yana da matukar tayarda hankali.
Alhaji Abubakar Sadiq sakataren Miyetti Allah reshen jihar Neja yace akwai matukar bukatar ganin hukumomi sun sanya idanu a kansu.Kwararowar bakin Fulani daga jihohin zuwa Neja babbar matsala ce.
Matsalolin da aka samu tsakanin makiyaya da manoma a wasu jihohin arewa bakin Fulani dake shigowa kasar da basu san al'adun Najeriya ba suke haddasa rigingimu.Kamata ya yi gwamnatocin tarayya da jihohi su tashi tsaye.
Yakamata gwamnati ta samarma Fulanin da suka gudo matsuguni domin idan Boko Haram ta raba mutane da muhallansu gwamnati na samar masu matsuguni.
Da alama Fulani sun rabu kashi biyu. Akwai wadanda aka sace masu shanu da yanzu suna jihar Neja. Irinsu suna bukatar taimako. Akwai wasu kuma da halayensu suka tilasta masu yin kaura. Idan ba'a lura ba zasu cigaba da mugayen halayensu a jihar.
Wasu 'yan gudun hijiran sun ce sun fito ne daga jihar Zamfara saboda yawan sace masu dabbobi da ake yi. Barayi dake sace masu shanu sun yi yawa. Cikin kwanaki goma an sace fiye da garke talatin na shanu.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5