Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Satar Shanu da Bata Gonaki Ke Haddasa Rikici a Jihar Filato


Shugabannin addinai akan hadin kai da zaman lafiya
Shugabannin addinai akan hadin kai da zaman lafiya

Matasan karamar hukumar Lantang ta Kudu sun kuduri aniyar bin hanyoyin da doka ta ayyana domin samun saukin tashin hankali a yankinsu

Furucin matasan ya biyo bayan ziyarar da kwamitin sasantawa na majalisar dokokin jihar ya kai yankin saboda jin bahasi da samun hanyoyin zaman lafiya a jihar.

Shugaban matasan John Zimfa yace matsalar satar shanu da barnata gonaki suke haddasa tashin hankali a jihar. Sun zauna a yakinsu sun kuma umurci mutane idan shanu suka yi barna to kada su ce zasu je su kwashe shanun su bi hanyar doka.

Sarakunan gargajiya na yankin sun bukaci gwamnatin jihar da ta nada masu babban sarki da zai iya tsawatawa duk wanda ya yi laifi kasancewa shekaru 21 ke nan basu da sarki.

Kwamitin ya yada zango a karamar hukumar Lantang ta Arewa inda basaraken gargajiya Ponzi Zimi Nimlong Lamin ya bayyana rashin jin dadinsa da yadda siyasa ta hana kawo zaman lafiya a jihar. Yace rashin aiwatar da doka ya zama babban matsala.

Basaraken ya jaddada batun yiwa babura da ake anfani dasu a kauyuka rajista da gina hanyoyi da samarda layin wayar tarho da kawarda shingayen da jama'a ke sawa bisa hanya ba kan ka'ida ba.

A karamar hukumar Mangu kuma kwamitin ya gana ne da al'ummar garin Kadunu da aka kaiwa hari a ka kashe mutane tare da kone gidaje. Dagacin Kadunu Muhammad Ismail Bayero yace an kashe mutane daban daban yana mamakin manufar lamarin. Ya roki a sa masu sojoji tsakaninsu da Barkin Ladi.

Shugaban kwamitin kuma mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Yusuf Adamu Garji yace suna kan tattara bayanai domin bada shawarwari da zasu kawo zaman lafiya.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG