Majalisar Dinkin Duniya t ace sama da mutane 15,000 sun tsere daga kudancin Sudan don guje way akin da ake a yankin Abyei da ake takaddama akai.
Shugaban Hukumar Kare ‘Yancin Dan Adam Ta Majalisar Dinkin Duniya Navi Pillay ya yi Allah wadai da tashin hankalin a cikin jawabinsa na yau jiya Talata sannan ya shawarci arewaci da kuduncin Sudan su sasanta don kawo karshen tashin hankalin.
Dakarun arewacin Sudan sun mamaye yankin mai arzikin man fetur, wanda da arewa da kudun da kwanan nan za ta sami ‘yancin gashin kai, kowannen ke ikirarin nasa ne. Shaidu sun bayar da rahoton kone-kone da wasoson gine-gine a garin Abyei ran Litini.
Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce suna kokarin tantance yawan masu bukatar taimakon gaggawa ran Litini to amman ya zame masu tilas su kaurace wa Agok lokacin da aka shiga harbe-harbe.
Shugaban hukumar ta kare ‘yancin dan adam Pillay na kiran da a tattauna don kawo karshen tashin hankalin don kuma, kamar yadda y ace, a kauce wa fadawa cikin rigingimu da rudami mafiya muni.
Fadan na Abyei ya tayar da fargabar yiwuwar sake fadawa cikin yakin basasa. Da arewa da kudu sun yi yaki na tsawon shekaru 21, da aka kawo karshensa a 2005, bayan bangarorin biyu sun gwabza kan yankin Abyei, da sassan yankin masu ni’ima da kuma arzikin man fetur.