Ranar Litinin din nan maharan suka kama madafin ikon garin duk da cewa garin na kunshe da jami'an tsaro da dama.
Amma mafi yawan jami'an tasron sun arce zuwa Kamaru domin kaucewa gamuwa da maharan. Maharan dai suna cigaba da yadda suke so ba tare da samun wata turjiya ba daga jami'an tsaron Najeriya.
'Yan Boko Haram din sun soma ne da kaiwa jami'an tsaro hari musamman sojoji tare da bayyanawa jama'ar garin cewa ba dasu suke yi ba su kwantar da hankalinsu. To amma daga bisani sun dawo sun juya kan mutanen garin suna kashe mutane musamman matasa tare da fasa shaguna da yin awongaba da kayansu.
Wani jami'in tsaro da ba na soja ba wanda kuma bai yadda a ambaci sunansa ba yace suma sun tsallaka zuwa kasar ta Kamaru domin tsira da rayukansu. Da farko 'yan bindigan sun yiwa mutane wayo da fada masu su kwantar da hankalinsu amma bayan sun tabbatar cewa garin na hannunsu sai suka koma kan mutanen garin suna kashesu.
Mutane manya da maza da mata da yara suna nan zube a kasar Kamaru sun zama abun tausayi domin babu taimako daga koina. Lamarin ya jefa tsoro cikin zukatan mutane ganin yadda kungiyar ta Boko Haram ke kara karfi. Kawo yanzu banda kauyukan da da can kungiyar ta kame akwai wasu manyan garuruwa a hannunta.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.
Your browser doesn’t support HTML5