Firayin ministan kasar Australiya Malcolm Turnbull ya sha da kyar daga wani kalubalen shugabanci da ya fuskanta cikin jam’iyyar sa ta Liberal mai ra’ayin ‘yan mazan jiya.
Turnbull ya yi kira akan a kada kuri’ar zaben sabon shugaban jam’iyyar yau Talata, kwana daya bayan da yayi watsi da shirinsa na yin doka akan kudurin takaita amfani da iskar gas mai gurbata yanayi a kasar, bayan wani bore da masu tsattsauran ra’ayin jam’iyyar sa suka yi.
Ministan cikin gidan Australiya Peter Duntton, wanda ya dauki alkawarin ba Turnbull cikakken goyon baya jiya litinin, shi ya kalubalanci firayin ministan a zaben. Dan majalisar dokoki daga jam’iyyar Liberal, Nola Marino ya ce Turnbull ya sami galaba akan Duntton da kuri’u 48 yayinda Duntton ya sami kuri’u 35. Duntton ya sauka daga mukaminsa a majalisar zartaswar kasar bayan da aka yi zaben ya koma a matsayin dan jam’iyya kawai, amma ana sa ran zai sake kalubalantar Turnbull akan shugabancin majalisar zuwa Alhamis.
Wannan kalubalen shugabancin da Turnbull ya fuskanta na zuwa ne a yayinda ra’ayoyin jama’a akan farin jin jam’iyyar Liberal suka nuna cewa jam’iyyar na bayan jam’iyyar adawa ta Labor sosai, gabanin zaben ‘yan majalisa da za a yi a watan Mayun shekara mai zuwa