Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Duniya Na Ta Ta'aziyyar Rasuwar Kofi Annan Tare Da Jinjina Masa


Marigayi Kofi Annan
Marigayi Kofi Annan

Yabon gwani ya zama dole: bayan rasuwar tsohon Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, ya na ta shan yabo saboda abin koyi da dama da ya yi a duniya.

Jinjina da ta’aziyya na ta kwararowa daga sassa dabam-daban na duniya, game da tsohon Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan, wanda ya rasu jiya Asabar bayan wata ‘yar gajeruwar jinya, ya na mai shekaru 80 a duniya.

Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya na yanzu, Antonio Guterres, ya bayyana marigayi Annan da “abin koyi wajen ayyuka na gari” ya kara da cewa, “Kofi Annan ya kasance Majalisar Dinkin Duniyar kanta, ta fuskoki dabam-dabam.”

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo ya ba da sanarwar ware mako guda na makokin abin da ya kira, “Daya daga cikin ‘yan kasa mafi shahara” sannan ya yi nuni da cewa Annan ya kasance mutumin da ya yi matukar imanin cewa, mutanen Ghana na da kokarin shata ma kansu lawali mai fa’ida da kawo cigaba.

Tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya ce Annan ya kasance kwararren jami’in diflomasiyya mai son agazawa wanda yayi aiki tukuru a Majalisar Dinkin Duniya. .

Ita ma Jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley, ta ce Annan ya sadaukar da ransa wajen kokarin mai da duniya wuri mai cike da salama, ya na mai kare mutunci kowani dan adam.

Wadannan kalaman sun yi mawafaka da na Shugaban kungiyar Tarayyar Turai Jean Claude Juncker da sauran masu fadi a ji a duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG