Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Kwace Wata Gunduma A Faryab Dake Kudancin Afghanistan


Mayakan Taliban
Mayakan Taliban

Rahotanni sun ce mayakan kungiyar Taliban sun mamaye wata gundumar a cikin lardin Faryab dake kudancin Afghasnistan kuma sun kama sojojin gwamnati da dama.

Fadar ta yau Lahadi na zuwa ne bayan kashedin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi a kan kaiwa ma’aikatan agaji hari a cikin kasar ya kai kashi 20 cikin dari a wannan shekara, kuma an kashe ma’aikatan agajin 23, wasu 37 suka ji rauni, yayin da aka kuma yi garkuwa da wasu 74.

Gwamnan lardin Faryab, Nahgibullah Fayiq, ya fadawa Muryar Amurka cewa gundumar Bilchiragh ta huskanci hare hare kwanaki da dama kuma jiya Asabar ta shiga hannun yan ta’addan, saboda dakarun tsaron Afghanistan da aka mamaye a wurin basu samu karin taimako ba.

Gwamnan yaki yin wani karin bayani a kan hali da dakarun gwamnatin ke ciki. Kafafen yada labarai na cikin gida sun ce kimanin sojojin Afghanistan 100 suka bace ba a gansu ba.

Mai Magana da yawun kungiyar Taliban, yace mayakansu sun shiga gundumar ba tare da samun turjiya daga dakarun gwamnatin ba, da wani zub da jini ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG