Trump da Abe ba bakin juna bane. Firayin ministan Japan shi ne shugaban wata kasa da shugaban Amurka ya taba ganawa da shi ido-da-ido ya kuma yi magana da shi a lokuta da dama.
WASHINGTON D C —
Shugaban Amurka Donald Trump ya karbi bakuncin Firayin ministan kasar Japan Shinzo Abe da safiyar yau Talata don ganawar kwanaki biyu, fadar White House ta ce tana sa ran tattaunawar zata yi tasiri sosai.
Da take magana da manema labarai daga cikin jirgin shugaban Amurka Air Force One zuwa jihar Florida, sakatariyar yada labaran fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta ce tattaunawar da za a yi tsakanin shugabannin biyu za ta ta’allaka ne akan shirye-shiryen ganawa da Koriya Ta Arewa, da kuma batun cinikayya.
Trump da Abe na da babban kalubale da ya shafe su, batun Koriya Ta Arewa, wadda ke shirin makamai masu linzame da na nukiliya da suka saba wa takunkumin Majalisa Dinkin Duniya.