Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Bincike A Amurka Da Birtaniya Sun Kirkiro Sinadarin Nakar Da Roba Cikin Gaggawa


Koina a duniya roba na cika teku ko juji amma yanzu sinadarin da aka gano zai yi maganinta
Koina a duniya roba na cika teku ko juji amma yanzu sinadarin da aka gano zai yi maganinta

Bisa kuskure wasu masu bincike a Amurka da Birtaniya sun kirkiro wani sinadarin da zai narakar da roba cikin gaggawa fiye da abun da aka saba gani

Kimanin ton miliyon takwas na robobi ne suke karewa a cikin teku a fadin duniya a kowace shekara, amma wani tuntube a dakunan bincike na kimiyya ya baiwa masana kimiya kwarin gwiwan shawo kan wannan barazana ga duniya.

Masu bincike a Amurka da Birtaniya sun ce sun kirkiri wani sanadari bisa kuskure, wanda zai iya narkar da roba cikin gaggawa fiye da sinadarin da ake amfani da shi wurin narkar da ita a yanzu.


Sun cimma hakan ne ta hanyar kara karawa sinadarin-guba da ake kira "amino acid" da turanci da nufin rage kaifinsa, amma sai akasin haka ya faru.


Masu binciken sun ce burinsu shine su kara yin kwaskwarima ga abunda suka ganon, ta yadda za'a rika narkar da roba kwatankwacin aikin masana'antu wajen kere-kere.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG