Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanatoci 4 Daga Jam'iyyun Democrat Da Republican Sun Gabatar da Kudurin Yin Allah Wadai Da Kungiyar Boko Haram


Senator Elizabeth Warren daya daga cikin wadanda suka gabatar da kudurin yin Allah wadai da kungiyar Boko Haram
Senator Elizabeth Warren daya daga cikin wadanda suka gabatar da kudurin yin Allah wadai da kungiyar Boko Haram

Ranar 14 ga wannan watan ranar da 'yan matan Chibok suka cika shekaru hudu a hannun 'yan kungiyar Boko Haram da suka sacesu daga makarantarsu, wasu sanatoci hudu daga jam'iyyun Democrat da Republican sun gabatar da kudurin yin Allah wagai da kungiyar a Majalisar Dattawan Amurka

Wasu Sanatoci 4 na majilisar dattijan Amurka daga manyan jam'iyun nan biyu, sun gabatar da kuduri da yayi Allah wadai da kungiyar Boko Haram da cikar shekaru hudu da sace 'yan mata 'yan makaranta a makarantar sakanadare dake garin Chibok, a jahar Barno.

Senatocin sun hada da Tammy Balwin ta jamiyyar Democrat daga jihar Wisconsin, da Susan Collins, ta jamiyyar Republican daga jihar Maine, da Dick Durbin dan jam'iyyar Democrat daga jihar Illinois,da kuma Jeane Shaheenna 'yar jamiyyar Democrat daga jihar New Hampshire, sai kuma Elizabeth Warren 'yar jam'iyyar Democrat daga jihar Massachussets.

Sanatocin a cikin wata sanarwar hadin gwuiwa sun yi ALLAH Waddarai da Boko Haram, tare da kiran gwamnatin Amurka da ta Najeriya da su dauki matakai na musamman da za su kawo karshen kungiyar ta ta’addanci.

Ranar 14 ga watan Afirilu na wannan shekarar ‘yan matan Chibok da aka sace suka cika shekara 4 a hannun wadanda suka sace su.

Ko baya ga wadannan ‘yan matan da aka sace a makarantarsu a garin Chibok haka kuma da yawan ‘yan Najeriya sun bata wasu kuma suna hannun ‘yan Boko Haram din.

Wannan kungiyar ta Boko Haram ta kware wurin kai hari iri daban-daban akan ‘yan Najeriya da basuji ba basu gani ba, musammam ma matan da suke zuwa karatun boko.

Yau wannan kungiyar ta Boko Haram ta zame wata babbar barazana ga farar hula a Najeriya, dama harkokin tsaro a yankin kasar, har ma da muradun Amurka.

Don haka wannan barazanar da tashin hankalin da take cusa matasa da ‘yan mata tana neman ta wuce gona da iri wanda tilas ne a dakatar da ita inji Sanata Balwin.

Tace tilas ne Amurka da gwamnatin tarayyar Najeriya su shige sahun gaban kasashen duniya domin daukar matakin ganin an ci karfin wannan kungiyar, tare da samun tabbacin matasa a Najeriya suna iya zuwa makaranta domin samun ilmi.

Ita dai wannan kungiyar ta Boko Haram ta gudanar da mummunar gallazawa mutane tareda sace mata, da ‘yan mata dama yara kanana kana tayi sanadiyyar mutuwar dubban mutane ciki ko harda wasu wuraren da suke matattaran farar hula ne musammam a arewa maso gabashi da tsakiyar Najeriya a shekarun da suka gabata.

Sanata Collins tace da zarar an aiwatar da tsarin na hadin gwuiwa na tsawon shekaru 5, wanda yayi bitar sa shekaru biyu da suka gabata, to ba shakka wannan zai aike da sako cewa ba za a taba mantawa da ‘yan matan Najeriya ba wadanda aka gallaza mawa domin kawai sun zabi su samu ilmi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG