Firaiministan Bahamas, Hubert Minnis, ya bayyana jiya Lahadi da, a ta bakinsa, “rana mafi muni a rayuwata” yayin da mahaukaciyar guguwar nan da aka yi wa lakabi da Hurricane Dorian ta abkawa tsibirin da ake ganin ita ce guguwa mafi karfi da ta bullo a yankin na Atlantika cikin shekaru 84.
WASHINGTON DC —
“Mutane da dama sun ki jin gargadin. Wasu mutanen kuma an barsu a baya, da kuma wadansu daidaiku a wajejen yankin West End wadanda su ka ki barin wurin,’ a cewarsa a taron manema labarai a Nassau. Ya kara da cewa, “Abin da zan iya fada masu kawai shi ne ina fatan ba wannan ne karo na karshe da za su ji muryata ba.”
Mahaukaciya Guguwar da aka yi wa lakabi da Dorian ta abkawa tsibirin Great Abaco a Bahamas da kuma tsibirin Grand Bahama inda mahukaciyar guguwar ta kai mataki na 5, da ta ke tafe da iska mai gudun kilomita 295 a cikin sa’a daya.