Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Firayim Ministan Burtaniya Yayi Yunkurin Rage Tsawon Wa'adin Zaman Majalisar


A yau Laraba, Fira Ministan Burtaniya Boris Johnson ya bayyana wani yunkurin sa na rage tsawon wa'adin zaman majalisar, kafin 31 ga watan Oktoba, ranar da Burtaniyya za ta fice daga Tarayyar Turai.

Johnson ya ce, ya nemi Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth ta kawo karshen zaman majalisar na yanzu, sannan kuma zai gabatar da wani sabon zaman tare da Jawabin Sarauniyar a ranar 14 ga watan Oktoba, tare da bayyana kudirin majalissar ga gwamnatin.

Kakakin Majalisar Wakilai John Bercow, ya ce, kudirorin Johnson "karya dokar tsarin mulki ne," kuma ya ce ainihin abin da ya faru "shi ne dakatar da yin muhawara a majalisar ta Brexit da kuma aiwatar da ayyukanta na daidaita tafarkin kasar."

Johnson ya yi alkawarin fitar da Birtaniyya daga Tarayyar Turai ko da ba’a samu yarjejeniyar janyewa ba, wacce ke fayyace sharuddan ficewar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG