Firai ministan kasar Pakistan yace wasu na nan suna kulla mishi makircin ganin bayan gwamnatinsa, a daidai lokacinda gwamnatin tashi ke shan sukar lamiri saboda rahottanin da ake watsawa na cewa wai ta aikowa Amurka wata takardar asiri, tana rokon a taimaka, a hana yi mata juyin mulki.
A yau ne Firai Minista Yousuf Raza Gilani yake wannan kalamin bayanda babbar Kotun Kolin Pakistan ta bada sanarwar cewa zata yanke shawara akan ko ta binciki wannan lamari ko ta kyale shi.
Ance tun cikin watan Mayun da ya gabata wani babbar kusa na gwamnatin shugaba Asif Ali Zardari ya aiko wannan wasikar inda ake neman Amurka ta taimaka wajen tarwatsa wani yunkurin juyin mulkin da aka ce sojan Pakistan na kitsawa jim kadan bayan harin da Amurka ta kai a can Pakistan har ta kashe tsohon madugun al-Qaida, Osama Bin Laden.
Tun daga lokacin ake ta kira akan shugaba Zardari da pr.minista Gilani da suyi murabus