Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan ta'adda ne, sun kai hari kan wassu kauyuka uku da suka hada da Bikutu da Zurak a karamar hukumar Wase dake jahar Filato, inda suka hallaka mutane da dama, wasu da dama kuma suka jikkata.
Wani mazaunin yankin da ya bukaci a sakaya sunansa saboda tsaro yace 'yan ta'addan sun zo ne kan babura da yammacin jiya Litinin suka yi aika-aikar kuma har yau Talata suna kan taruwa a kauyen Sabon Gari don sake kaiwa hari.
Malam Ahmad Aliyu, limamin babban masallacin garin Zurak yace suna bukatar dauki daga jami'an tsaro.
Hukumomin tsaro basu tabbatar da harin ba ko adadin wadanda suka rasa ransu da wadanda suka jikkata.
Shugaban karamar hukumar Wase, Hamisu Anani, a hirarsa da Muryar Amurka jim kadan kafin harin yace suna daukan matakan samar da tsaro a yankin.
Yankin na Zurak dake zama babbar wuri da ke da albarkatun ma'adinai na kwalli, ya sha fama da ayyukan 'yan ta'adda, wanda ko a watan jiya hukumomin tsaro suka karya laggon wassunsu.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5