ABUJA, NIGERIA - Janar Buba wanda ke wannan batu a taron manema labarai a Abuja ya ce koda yake ba lalle ya zama suna da maslahar baki daya na matsalolin ba, amma duk da haka ya tabbatar da cewa sojojin kasar suna nan suna aiki wurjanjan don kawo karshen wannan matsala.
Yana mai tabbatar da cewa ba shakka za a cimma manufa don samar da kwanciyar hankali a ko'ina cikin kasar.
Sojojin Najeriya, a cewar Janar din, sun kudiri aniyar rugurguza cutar kansar da ke son zama karfen kafa a sha'anin tsaron kasar da ta kai ga an sami irin abin bakin cikinnan da ya faru a jihar Filato.
Ya kara da cewa tuni an aike da zaratan dakaru da kayan aiki zuwa duk sassan da ake ganin matsalar tsaro ka iya faruwa don tabbatar da cikakken tsaro.
Masana tsaro irinsu Air Commodore Baba Gamawa mai ritaya na mai cewa lalle halin da ake ciki a Najeriya na bukatar hadin kan dukkan ‘yan kasa don shawo kan wannan matsalar.
Saurari cikakken rahoto daga Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna