SOKOTO, NIGERIA - Daga cikin masu kalubalantar gwamnati akwai cibiyar nazarin ci gaban addinin Musulunci ta Najeriya dake Zariya wadda a karshen taron ta na kasa da ta yi a jihar Kebbi, ta yi Allah wadai akan kisan da aka yi wa jama'a a Filato, tare da kalubalantar gwamnati akan kawo karshen yi wa jama'a kisan kiyashi, da dai wasu kalubale da suka dabaibaice kasar.
Kalubalen da suka yi wa Najeriya tarnaki sun jima suna mayar da hannun agogo baya da kawo koma bayan kasar a sassa daban-daban duk da yake mahukunta su ma sun jima suna cewa suna daukar matakan shawo kan kalubalen.
Daga cikin su, kisan kiyashi da ake yi wa jama'a na daga cikin abubuwan da watakila suka fi daukar hankalin 'yan kasar, kamar yadda kasa da wata daya aka yi asarar daruruwan rayukan jama'ar da basu-ji-ba-basu-gani-ba a jihohin Kaduna da Filato.
Cibiyar nazarin ci gaban addinin Musulunci ta Najeriya a karshen taron da ta gudanar a wannan shekara, ta bi sahun masu yin Allah wadai akan kisan na baya-bayan nan a jihar Filato, tare da kalubalantar gwamnati a kan kawo karshen wadannan matsalolin.
A hirar shi da Muryar Amurka, Farfesa Siraj Abdulrahman shugaban kwamitin shirya babban taron na cibiyar ya ce, harin da ya yi sanadin salwatar daruruwan rayukan abin takaici ne, kuma ya zamo dole gwamnati ta nuna da gaske take yi wajen magance irin wadannan matsalolin.
Ya ce, "ko abinda ya faru a Tudun Biri dake jihar Kaduna har yanzu gwamnati ta kasa gamsar da 'yan kasa akan matakin da zata dauka na hukunta masu hannu ga wannan harin."
Rashin yin hukunci akan masu aikata manyan laifuka har ma dai na kisa na daga cikin abubuwan da jama'a ke nuna yatsa akan gwamnati har suna ganin cewa shi ke sa ba'a daina aikata irin wadannan laifukan ba.
To sai dai a mahangar masana lamurran shari'a ba wannan ne kawai matasla ba, domin yanzu haka ba za'a rasa wadand aka yankewa hukuncin kisa ko daurin rai-da-rai ba.
A bayaninsa, Barrister Muhammad Mansur Aliyu masanin lamurran shari'a a Najeriya na ganin daga cikin matsalolin da ke sa ake ganin gwamnati ba da gaske ta ke yi ba, akwai rashin kama masu laifin da ya kamata a kama su, ko kuma rashin tattarawa da gabatar da kwarararn shaidu da zasu bayar da damar a yi hukunci ga masu laifi, da kuma wasu matsaloli da ba za'a kaucewa cin karo da su ba a haujin masu shari'a.
Wadannan da ma wasu kalubale kamar rashin samun kyakkyawan shugabanci, fatara, rashin aikin yi, tabarbarewar ayyukan noma, hadin kan 'yan kasa da sauransu, na daga cikin abubuwan da kungiyoyi da daidaikun jama'a ke fafutukar taimakawa ganin an magance, inda wannan cibiyar ta nazarin ci gaban Musulunci na taron ta karo na 26 a wannan shekara ta mayar da hankali wajen jawo hankalin 'yan Najeriya masu shugabanci da wadanda ake shugabanta.
Kungiyoyi da hukumomi dai sun jima suna bayar da gudunmuwa ta hanyoyi daban-daban akan yadda Najeriya zata iya kasancewa bisa kyakkyawar turba, sai dai har yanzu a iya cewa kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu, duk da yake wasu kungiyoyin basu yi kasa a guiwa ba ga kokarin da suke yi, ko yaushe ne Najeriya zata hau tudun mun tsira lokaci ne kawai zai nuna.
Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:
Dandalin Mu Tattauna