Maharan sun kone gidaje 25 tare da sace Shanun mazauna kauyukan da wasu kayayyaki, a cewar Yakubu Pam, wani mazaunin yakin. Ya kuma tabbatar da cewa yanzu haka akwai mutanen da yanzu haka suka rasa muhallansu basu da wajen da zasu kwana. Haka kuma ya yi korafin cewa babu ko da jami’in tsaro daya a wajen da wannan lamari ya faru.
A bangare guda kuwa, sakataren kungiyar Miyetti Allah a karamar hukumar Barikin Ladi, Abubakar Gambo, yace suma kusan kwanaki uku kenan ake sace musu Shanu, wanda ya zuwa yanzu an sace Shanun sama da dubu.
Hukumar ‘yan sandan jihar Filato ta tabbatar da mutuwar mutane Takwas a yankin, a wata sanarwa da mai magana da yawun ‘yan sandan na jihar, Terna Tyopev, ya aikawa manema labarai ta ce tuni suka tura jami’ansu yankin domin tabbatar da tsaro da bankado wandanda suka aikata aika-aikan.
Itama gwamnatin jihar Filato, ta bakin kwamishinan yada labarunta Yakubu Datti, ta jajantawa al’ummar yankin bisa abin da ya faru, haka kuma gwamnati ta nemi jami’an tsaro da su gano wadanda suka aikata kisan domin su fuskanci hukunci.
Domin karin bayani saurari rahotan Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5