Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan Nigeria Sun Yi Wa EFCC Korafi Kan Yadda Kamfanonin Waje Ke Hana Su Aiki


Wasu kungiyoyin matasan Nigeria sun yi gangamin mika korafinsu ga hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC, kan yadda ake hanasu aiki amma kuma sai a kai ayyukan kasashen waje.

Yayinda suke gangami matasan na cewa akwai kwararrun matasa injiniyoyi da makamantansu a Nigeria amma an hanasu damar ba da tasu gudummawa wajen ci da kasar gaba.

Matasan na cewa ayyukan da suka dace a yi cikin gida sai a kai su can Koriya ta Kudu inda matasansu injiniyoyi ke anfana.

Daya daga cikin masu jagorar gangamin zuwa hukumar yaki da cin hanci da rashawa, EFCC, Moses Siyasiya, yace hanasu ayyukan da za su iya yi, ya sa su zama ‘yan kallo a kasarsu.

Wata kungiyar matasa mai suna Connected Development ita ce ta shirya gangamin. Hamza A. Lawal ne kuma shugaban kungiyar tare da hadin kan kungiyar matasa kwararru a fannonin ilimi.

Kungiyoyin biyu sun mika wasikar korafinsu ga hukumar EFCC inda suka bukaci a gudanar da bincike akan lamarin saboda matasa su samu damar baza kolin irin basirar da Allah ya basu. Matasan na ganin abun dake faruwa tamkar cin hanci ne da rashawa.

Bilkisu Ahmed jami’ar yada labarum kungiyar gwagwarmayar ta ce bai kamata a ce ‘yan kwangilar kasashen waje su zo Nigeria su dauki kwangila su kai wasu kasashen ba. Amma ga matasan Nigeria basu da aikin yi. Ta ce ‘yan jarida su taimaka su yada abun dake faruwa domin a jawo hankalin gwamnatin kasa ta yi abun da ya dace. Ta yi misali da kamfanin man Nigeria.

A saurari rahoton Hauwa Umar Udubo domin karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG