Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shin Za a Mika Korafe-Korafen 'Yan Rohingya Ga Kotun ICC?


Wasu matan Rohingya suke kuka yayin da a ke taron cika shekara guda da irin ukubar da suka fuskanta a Myanmar a bara
Wasu matan Rohingya suke kuka yayin da a ke taron cika shekara guda da irin ukubar da suka fuskanta a Myanmar a bara

Yanzu haka, kasashen duniya da dama, sun zuba ido su ga matakin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai dauka, bayan da wani rahoton kwamitin binciken kwakwaf na Majalisar da aka fitar a ranar Litinin ya nemi a mika batun ga kotun hukunta manyan laifuka ta ICC.

Tun bayan da wani kwamiti na musamman ya gudanar da wani bincike kan korafe-korafen cin zarafin da ake zargin dakarun Myanmar sun aikata akan Musulmi 'yan kabilar Rohingya, jama'a da dama suka zuba ido su ga abin da zai biyo baya.

Sakamakon binciken, wanda aka fitar a ranar Litinin ya ba da shawarar a binciki a kuma tuhumi babban hafsan sojin kasar bisa zargin aikata laifin kisan kare dangi akan ‘yan kabilar ta Rohinya.

Rahoton binciken ya lissafo wasu janar-janar na soji guda shida wadanda ake zargi na da hannu dumu-dumu a wannan aika-aika.

Daga cikinsu har da babban kwamandan dakarun kasar, Gen. Min Aung Hlaing, kamar yadda wakiliyar Muryar Amurka, Margaret Basheer ta ruwaito a rahotonta.

Sama da Musulmi ‘yan kabilar ta Rohingya 700,000 suka tsere daga jihar Rakhine, bayan wani farmaki da dakarun kasar suka kaddamar akansu a watan Augustan bara.

Sakamakon binciken har ila yau, ya nemi a binciki da yawa daga cikin kwamandojin babban hafsan sojin a kuma tuhume su da laifukan kisan kiyashi da ake zargin sun aikata akan ‘yan kabilar ta Rohingya.

Musulmin 'yan kabilar ta Rohingya, sun kasance tsiraru a kasar ta Myanmar mai mabiya addinin Bhudda da ke da rinjaye.

Sai dai rahoton, ya yi kira ga kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya mika wannan batu ga kotun hukunta manyan kaifuka ta ICC da ke Hague.

“Binciken da muka yi, ya tabbatar mana da cewa akwai bukatar a gudanar da binciken aikata manyan laifuka a kuma tuhumi wadanda ake zargi, musamman janar-janar din sojojin kasar da aka fi sani da Tatmadaw.” A cewar Christopher Sidoti, wanda shi ma mamba ne a kwamitin da ya gudanar da binciken.

Akan zargi kotun ta ICC da amyar da hankali kan kasashen Afirka wajen irin shari'ar da ta ke saurare. Ko da yake, kotun ta sha musanta hakan.

A lokacin harin, wanda aka kwashe watanni ana kai wa, ‘yan kabilar ta Rohingya, sun tsere zuwa Bangladesh da ke makwabtaka cikin yanayi na matsananciyar yunwa inda suka rika ba da labarin irin ukubar da suka fuskanta.

“Irin abin da ya faru, wata dabara ce da ake amfani da ita a yaki, mun kuma gano cewa an aikata fyade har da na taron dangi, bautarwa ta hanyar yin lalata, da kuma tilasta musu su yi tsirara da guntule sassan jiki.” Inji daya daga cikin mambobin kwamitin da suka yi bincike, Radhika Coomaraswamy.

Binciken ya kuma kara bayyana cewa, harin da dakarun kasar suka kai, martani ne ga wani hari da wasu tsagerun ‘yan Rohingya suka kai akan jami’an tsaro, lamarin da ya kai ga mutuwar wasu daga cikinsu.

Sai dai kamar yadda sakamakon binciken ya nuna, martanin ya yi tsauri da yawa, kuma ga dukkan alamu an shirya shi ne.

Su dai hukumomin kasar ta Myanmar, sun sha musanta yadda ake kwatanta hare-haren.

“Mun sha fada, wannan ba kisan kare dangi ba ne, irin wannan zargi na bukatar kwararan hujjoji, saboda haka, muna musanta yadda ake danganta dakarun kasarmu da wannan aika-aika.” Inji jakadan Myanmar a zauren Majalisar Dinkin Duniya, Hau Do Suan.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG