A ranar Litinin 16 ga watan Nuwamba ne kwamitin ya fara zaman sauraren korafin daga wadanda suka shigar da kara.
Sai dai kan karar da Barde Nelson Paul ya shigar na yadda sojoji suka far masa a gidansa da ya kai ga lalata masa dukiyoyi na miliyoyin Naira a gidansa, kwamitin ya ba da umarnin aikawa da rundunar sojojin Najeriya sammaci don ta amsa tambayoyi a gabanta.
Shugabar kwamitin, mai shari’a, Philomena Lot ta ba da umurnin a rubuta takardar dakatar da fansho na duk wani jami’in tsaro da ya yi ritaya ana kuma zarginsa da hannu kan cin zarafi ya kuma ki bayyana a gaban kwamitin.
Shugaban kungiyar lauyoyi na Jos, Barista Yakubu Bawa, ya ce duk wadanda suke ganin an ci zarafinsu sun dauki matakin cewa za su gabatar da korafe-korafensu a gaban kwamitin shari’ar ba tare da sun biya su ko kwabo ba.
Tsohon Sanata Shehu Sani daga jahar Kaduna ya ce matsalar Najeriya ba wai maganar yanar gizo ba ne ko zanga zangar EndSARS, ana yawan kashe mutane a arewacin kasar kuma gwamnatin da jami’an tsaro duk sun gagara daukan mataki.
Kuma kullum ana sace mutane sannan manoma ba su a arewacin Najeriya ba su isa su fita waje ba kamar kilomita daya ba’a sace su ba.
Sanata Sani ya kara da cewa yana goyon bayan zanga zangar lumana dari bisa dari amma ba ya goyon bayan yin fashe-fashe ko kona kayan jama’a da na gwamanati, kana ya yi kira da gwamnati ta yi adalci.
Hakimin Dargun, Aminu Mai Samari Dogo, ya ce ya kamata gwamnati ta samarwa matasa aikin yi domin rashin abin yi shi yake haddasa irin wadannan abubuwa.
Shi ma Garba Abdulkadir ya yi kira na musamman ga samari da su zauna da ‘yan uwansu da kuma ko wace kabilu a hada hannu a yi aiki don ci gaban kasa.
Gwamnan jahar Filato, Simon Lalong ya bayyana cewa jahar Filato ta yi asarar akalla Naira biliyan 75 a barnar da bata-gari suka yi loakcin zanga zangar kawo karshen rundunar 'yan sanda ta musamman da take yaki da muggan laifuka a Najeriya wato SARS, inda ya bukaci matasan da su nemi hanya da ba ta tashin hanakali ba domin gabatar da bukatunsu, kana ya yi alkawarin samar da hanyoyin ci gaba ga matasan jihar.
Saurari cikakken rahoton Zainab Babaji:
Your browser doesn’t support HTML5