Lamarin ya auku ne jiya bayan hatsaniyar da ta tashi tsakanin mazauna garin da sojoji yayinda da sojojin suka nemi kafa shingensu domin binciken matafiya akan hanya.
A cewar wani mazaunin garin Rwang Tengwom al'ummar garin sun nuna bijirewarsu ne da canza shingen 'yansandan kwantar da tarzoma da sojoji.
Yace su 'yan Heipang suna zaune sai ga sojoji sun zo a cikin motoci kirar hilux guda biyar da sunan zasu sa shinge, wato road block, a wajen sai mutane suka ce masu sun fi son 'yan sandan kwantar da tarzoma ba sojoji ba.
Suna cikin hayaniyar ke nan sai sojojin suka fara harbi tare da dukan wasu matasa. Lamarin ya sa mutane suna gudu. Mutane na gudu sojojin kuma na binsu har suka harbi wata mai goyo a gaban wani shago. Wata mata kuma ta fito daga gidanta ke nan sai ita ma sojoji suka harbeta a gaban kofar gidanta. Ita akan hanyar kaita asibiti ta mutu.
Mutanen garin sun ce babu wanda ya san batun kafa shingen. Sarkin garin da wakilansu a karamar hukuma da jiha basu da masaniya.
Jiya kuma da yamma da misalin karfe bakwai wai wata mota na wucewa sai aka yi harbi daga ciki wanda ya kashe mutane guda biyu da suke tsaye. Rwang yace lamarin na yamman ya nuna masu cewa dama can akwai wata manufa da sojojin suka zo dashi. Mutane hudu ke nan aka kashe a rana guda banda wasu biyu da aka ji masu ciwo.
Kakakin sojojin Keften Ikediji Iweha ya karyata batun cewa sojoji ne suka kashe matan biyu. Yace sakamakon canji da suka samu na gudanar da tsaro ya sa suka kafa shinge a mahadar Heipang, Barkin Ladi da Pendadi. Yace wasu gungun mutane suka ingiza matasa da mata su taso su hana kafa shingen lamarin da ya kai har suka dinga jifar sojoji da duwatsu da makamai masu hadari suka kuma rushe shingen.
Keften Iweha yace mutanen garin sun cigaba da tare hanya tare da kona tayoyi suna jifar motocin jama'a. A yunkurin kashe tarzomar jami'in soja daya ya samu rauni.
Ga rahoton Zainab Babaji.
Your browser doesn’t support HTML5