Ficewar Sojin Faransa Daga Burkina Faso Ta Haifar Da Ayoyin Tambaya

Sojojin kasar Faransa suna sintiri a kasar Ivory Coast.

A jamhuriyar Nijar masana sha'anin tsaro da jami’an fafutuka sun fara bayyana matsayinsu bayan da kasar Faransa ta yanke shawarar mayar da sojojin da ta kwashe daga Burkina Faso zuwa gida a maimakon sake girke su a kasashen Nijar da Cote d’ivoire kamar yadda aka ayyana a can farko.

Koda yake wasu na shawartar hukumomin Faransar su aika da wadanan sojoji zuwa Ukraine a wannan lokaci da yaki ke kara tsananta:

Dakarun musamman na Force Speciale kimanin 400 ne kasar Faransa ta girke a kasar Burkina Faso a matsayin wani bangare na matakan yaki da ta’addanci a yankin Sahel sai dai rashin ganin wani bayyananen sakamako ya sa gwamnatin rikon kwaryar Burkina Faso yanke shawarar kawo karshen ayyukan wadannan sojoji na rundunar Sabre wadanda da farko Faransa ta yi shelar za ta zo da su Nijar da cote d’ivoire amma kuma daga baya ta canza ra’ayi.

Mai sharhi akan lamuran yau da kullum mazaunin Faransa Seidik Abba na bin diddigin abubuwaan dake wakana a yankin Sahel.

Da yake bayyana ra’ayinsa akan matakin Faransar shugaban kungiyar Voix des sans voix Nassirou Saidou na cewa abu ne da ka iya haifar da gibi a fagen daga idan aka yi la’akari da yanayin tsaro da Burkina faso ke ciki a yau.

Jigo a kungiyar M62 Gamatche Mahamadou wanda ke farin ciki akan matakin soma ficewar sojojin da ya kira na mamaya daga yankin Sahel na ganin gwamnatin Macron ta yi kuskure domin a cewarsa a maimakon ta mayar da wadanan dakaru zuwa gida Ukraine ya kamata a aika su don ceto ta daga mamayar Russia.

A karshen makon jiya ne kasar Faransa ta fara kwashe askarawanta 400 daga Burkina Faso bayan shudewar wa’adin wata 1 da gwamnatin Cap Ibrahim Traore ta bayar akan bukatar wadanan sojoji na rundunar sabre su fice daga kasar.

Saurari rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

CECE KUCE KAN MATAKAN JANYE SOJOJIN FARANSA mp3.mp3