Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Sakamakon Yajin Aikin Ma’aikatan Hukumar NRC

Rigimar Daukar Jirgin Kasa A Kaduna

Yajin aikin gargadi na kwanaki uku da ma'aikatan hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya wato NRC suka yi ya hana zirga-zirgar jiragen kasa a fadin kasar.

Fasinjojin jirgin kasa na Abuja zuwa Kaduna; Legas zuwa Badun, da dai sauransu, sun makale a tashoshin jiragen kasan ne daga ranar Alhamis yayin da kungiyoyin jiragen kasa suka yi watsi da zuwa aikinsu na yau da kullum don neman gwamnati ta biya mu su bukatunsu na inganta walwalar ma’aikata.

Kungiyar ma’aikatan jirgin kasa ta Najeriya wato NUR da kungiyar manyan ma’aikata wato SSA sun fitar da sanarwar hadin gwiwa inda suka ce yajin aikin gargadi da suka fara a ranar Alhamis zai kare ne a ranar Asabar.

Jami’an kungiyoyin sun ce sun shiga yajin aikin da suke ci gaba da yi ne don aika sakon gargadi ga masu hannu da shuni da su biya bukatunsu na kyautata jin dadin ma’aikata da kuma inganta yanayin aikinsu.

Ma’aikatan da ke yajin aikin sun ce albashin da ake biyansu ya yi karanci kuma suna bukatar a yi nazari don yi musu kari zuwa sama inda kungiyoyin ke cewa rashin samar da mafita kan korafe-korafen su zai iya jawo yajin aikin gamagari na har illa Ma Sha Allah.

Rahotanni sun yi nuni da cewa tabarbarewar tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa na ‘yan kwanakin baya-bayan nan ya sanya jiragen kasa suka zama zabin hanyan sufuri ga ‘yan Najeriya da dama musamman daga Abuja zuwa Kaduna da Legas zuwa Ibadan da dai sauransu.

Rahotanni sun yi nuni da cewa yajin aikin hukumar NRC ya jawo asarar gomman miliyoyi yayin da kungiyoyin kwadagon ke ci gaba da yin yajin aikin kuma ana fargabar cewa asarar da hukumar NRC ke samu zai yi matukar tasiri ga kudden shigan ta da ma tattalin arzikin kasa kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ana iya tunawa, a cikin makwannin baya-bayan nan sai da hukumar NRC ta tsaida zirga-zirgan fasinjoji sakamakon yadda yan bindiga suka saka abubuwa masu fashewa a kan layin jirgin kasar lamar da ya yi barna kan titin jirgin.

A latsa wannan sauti don karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Fasinjojin Jirgin Kasa Sun Shiga Tsaka Mai Wuya Sakamakon Yajin Aikin Ma’aikatan Hukumar NRC